Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotun koli ta yi watsi da karar PDP da ke kalubalantar rashin cancantar Tinubu da Shettima

Published

on

Yayin da ya rage kwanaki uku a rantsar da sabon shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa Kashim Shattima, kotun kolin kasar nan ta yi watsi da karar da Jam’iyyar PDP ta shigar gabanta da ke kalubalantar rashin cancantar su ta zama shugabanni.

A zaman da kotun na yau wadda ta ke da alkalai biyar, ta ce jam’iyyar PDP ba ta gabatar da gamsassun hujjoji ba, wanda hakan ce ta sanya kotun yin watsi da karar.

Jam’iyyar PDP dai na cewa Jam’iyyar ta APC bai kamata ta tsayar da kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban kasa ba, duba da cewa ya nemi takarar sanatan Borno ta tsakiya a dai-dai lokacin da aka tsayar da shi mataimakin shugaban kasa, wanda hakan ya saba doka a Nijeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!