Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An wayi gari da ganin an tone wasu kaburbura a Dan-tsinke dake Kano

Published

on

A safiyar yau ne al’ummar unguwanni Dan-tsinke da Wailari dake karamar hukumar kumbotso a Jihar Kano, suka wayi gari da wani iftila’I, na shigar masu cikin makabartar yankin inda aka hake wasu kabururruka da kwashe wasu gawawwaki da aka binne.

Mai unguwar garin Ɗan tsinke Alhaji Sani Abdu ne ya tabbatar da hakan a safiyar yau inda yace suma sun wayi gari da ganin wannan lamari.

Wanda ya ce ‘sama da kabururruka hudu aka buɗe da kwashe wasu mamatan da ke ciki.

Da yake jawabi Shugaban kungiyar sintiri ta Vigilante Malam Ibrahim Umar Yaya, cewa yayi ‘yau da safe aka kira su zuwa makabartar cewa an ga wasu kabarurruka hudu a tone, wanda uku daga ciki an cere gawarwakinsu, an kuma bar likafanin, yayin da cikon na hudun kuma da gawar da likafanin duk an tafi dasu’.

Malam Muhammad Abdullahi Dan Sokoto guda ne cikin manyan dattawan yankin, yace ‘ya kamata mahukunta su shigo lamarin domin kawowa al’ummar yankin dauk’.

Suma mazauna yankin na Ɗan tsinke dai na nema hukumomin tsaro da mahukunta da su shigo ciki tare da kawo musu dauki domin kaucewa faruwar hakan nan a gaba.

Rahoton: Umar Abdullahi Sheka

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!