Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar dattawar Nijeriya ta amincewa Bola Tinubu karbo rancen Miliyan 800

Published

on

Majalisar Dattawar Najeriya ta amince da buƙatar shugaban ƙasar Bola Tinubu na karɓo rancen dala miliyan 800, don gudanar da shirin samar da tallafi ga masu ƙaramin ƙarfi a ƙasar.

Haka kuma Majalaisar ta yi gyara fuska ga dokar ƙarin kasafin kuɗin shekarar 2022.

Shugaban Majalisar Dattawan Sanata Godswill Akpabio ne ya karanto buƙatar shugaban ƙasar cikin wata wasiƙa da ya aike wa majalisar.

Tinubu ya bayyana cewa ‘majalisar zartarwa ta ƙasa ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ta amince da karɓo ƙarin rancen na dala miliyan 800 daga Bankin Duniya, domin aiwatar da shirin tallafin’.

Shugaban ya ce maƙasudin shirin, shi ne domin taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi don su samu abin biyan buƙataunsu na rayuwa.

Ko jiya Alhamis ma Shugaba Tinubu ya bayyana shirin gwamnatinsa na bai wa gidajen talakawan ƙasar nan miliyan 12, tallafin Naira Dubu 8 na tsawon watanni shida.

Rahoton: Ahmad Kabo Idris

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!