Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An yi bata-kashi da ƴan bindiga a Zariya

Published

on

Rahotanni daga garin Zaria na cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari a unguwar Low Cost, cikin daren jiya Lahadi inda suka yi garkuwa da mutane.

Wani mazaunin unguwar ya shaidawa Freedom Radio cewa, maharan sun ɓulla ne da misalin ƙarfe 11 na dare, inda suka riƙa harbe-harbe tare da yin garkuwa da wasu mutane.

Sai dai sun samu martani daga jama’ar gari da ƴan sintiri da kuma wasu jami’an tsaro.

Daga bisani an cafke mutum biyu daga cikin su.

Mun yi ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun ƴan sandan jihar Kaduna ASP. Muhammad Jalige, amma har kawo lokacin da muke haɗa wannan rahoto abin ya ci tura.

Yanzu haka dai al’ummar yankin na ci gaba da yin zaman ɗar-ɗar sanadiyyar harin.

Kuma har kawo asubahin Litinin ɗin nan Gwamnati da hukumomin tsaron jihar ba su ce komai ba a kai.

Jihar Kaduna dai na cikin jihohin da ke fama da hare-haren ƴan bindiga, wanda kuma lamarin ke ƙara tsamari a ƴan kwanakin nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!