Kaduna
An yi jana’izar fararen hula kusan 60 da yan Boko Haram suka kashe a Bama

An yi jana’izar fararen hula kusan 60 da yan Boko Haram suka kashe a garin Daral-Jamal na yankin Bama a jihar Borno.
Wadanda aka kashen sun hada da direbobi bakwai, yayin da mutum shida kuma leburori ne daga Maiduguri.
Rahotanni sun ce ‘yan ta’addan sun kona gidaje 20 da motocin safa 10 yayin da mazauna yankin suka tsere.
A ranar juma’ar da ta gabata ne dai mayakan na Boko Haram suka afka wa al’ummar wannan gari.
You must be logged in to post a comment Login