Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar yan sandan jihar Borno ta tabbatar da mutuwar mutane 6 a harin da Boko Haram ta kai yankin Jidari Polio jiya Alhamis

Published

on

Rundunar yan sandan jihar Borno ta ce akalla mutane shida ne aka kashe a wani hari da mayakan Boko Haram suka kai a yankin Jidari Polio da ke garin Maiduguri a Alhamis din da ta gabata.

Cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jihar ta Borno Mista Edet Okon ya fitar a yau Juma’a ta ce cikin wadanda al’amarin ya rutsa da su har da farar hula guda uku da kuma wani jami’in tsaron hadaka na JTF guda, sai kuma yan mata biyu da suka yi kunar bakin waken.

Sanarwar ta kuma ce wasu jami’an yan sanda da ke sashin yaki da yan fashi wato SARS da kuma wasu mutane bakwai sun samu muggan raunuka sakamakon harbin da yan ta’addan sukayi da kuma tada bama-bamai.

Okon ta cikin sanarwar ya kuma ce tuni rundunar yan sandan ta aike da Jami ‘anta domin kwantar da tarzoma da kuma kaucewa aukuwar sake kai wani harin.

Ya kuma ce Kwamishinan yan sandan jihar Mista Damian Chukwu na kira ga al’umma da su koma bakin ayyukan su na yau da kullum kamar yadda suka saba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!