Labarai
An yi jana’izar Marigayi Shiekh Dahiru Usman Bauchi

Dubunnan daruruwan mutane daga sassan Najeriya har ma da na kasashen ketare ne suka halarci taron jana’izar Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi da yammacin yau Juma’a a birnin Bauchi.
Fitattun mutanen da suka halarci jana’izar sun hada da Mataimakin shugaban Kasa Alhaji Kashim Shettima, da Gwamnan Kano Abba Kabir, da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, sai Gwamnan Neja Umaru Bago, da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu.
Haka kuma an gano da tsohon Gwamnan Bauchi Ahmed Muazu da Sanata Abdulaziz Yari da sauran wasu manyan yan siyasa da masu mulki da masu sarautun gargajiya na Najeriya har ma da na kasashen ketare.
You must be logged in to post a comment Login