Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Jigawa

An yi mummunan hatsarin mota a jihar Jigawa

Published

on

Wani mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu ‘yan gida daya a kan hanyarsu daga nan Kano zuwa karamar hukumar Malam Madori a Jihar Jigawa.

Wani dan uwan mamatan ya ce sun fito ne daga iyalin darakta mai kula da manyan makarantu a ma’aikatar ilimi ta Jihar JigawaHajiya Safiya Muhammad.

Mutanen sun rasu ne bayan da motarsu ta yi adungure a Danladin-Gumel da ke karamar hukumar Gumel a jiya asabar.

Nan take ne dai uku daga ciki suka mutu yayin da guda ta mutu bayan an kaita asibiti.

Sai dai da muka tuntubi rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa kan wannan mumunan hatsarin hakan mu bai jima ruwa kasancewar wayar mai magana da yawun rundunar Abdu Jinjiri ba ta shiga

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!