Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan bindiga sun kai hari a Kaduna

Published

on

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari yankin Buda dake karamar hukumar Kajuru cikin jihar Kaduna tare da kashe mutane uku.

Shugaban kungiyar mutanen yankin Awemi Maisamari ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an yi garkuwa da wasu da dama yayin harin.

Maisamari cikin wata sanarwar da ya fitar na cewa, harin ya faru ne a daren jiya Lahadi lokacin da mutane ke tsaka da bacci.

Harin na baya-bayan nan na zuwa ne, biyo bayan rahoton da Mai shari’a Isa Aliyu ya mikawa Gwamnan jihar ta Kaduna Nasir El-Rufa’i kan rikice-rikicen kudancin jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!