Connect with us

Labarai

An yi sulhu tsakanin KAROTA da masu adaidaita

Published

on

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC reshen jihar Kano ta cimma matsaya tsakanin ƙungiyoyin masu adaidaita sahu da hukumar KAROTA.

An cimma matsayar cewa, masu adaidaita za su ci gaba da biyan harajin Naira ɗari-dari a kullum.

Biyan farko zai zama ta banki, yayin da sauran kuma zai zamo ta na’urar cirar kuɗi ta POS da sauran wuraren hada-hadar kuɗi.

NLC ta kuma buƙaci masu adaidaita sahu da su janye yajin aikin da suke ciki nan take.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne ko ɓangarorin biyu za su karɓi sasancin da aka yi musu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,961 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!