Connect with us

Labarai

An yiwa ‘yan wasan Adamawa United Fashi

Published

on

An yiwa ‘Yan wasan tawagar Adamawa United da mukarraban su fashi da makami a hanyar Benin zuwa Ore, cikin daren Jumma’a.

‘Yan wasan na kan hanyar su ta zuwa wasan mako na 11, a gasar Firimiya ta kasa NPFL.

Tawagar ta Adamawa United, za ta fafata da takwarar ta, ta MFM FC da ke jihar Legas.

Lamarin ya faru da karfe 11:45 na daren Jumu’a, inda ‘Yan fashin suka ‘kwace wayoyi, kudade da sauran kadarori na ‘yan wasan da mukarraban su, tare da yin awon gaba da direban motar.

Rahotannin baya-bayan nan, da suka fito daga majiyyoyi daban-daban a Benin, sun ce ‘yan fashin sun bukaci a biya su naira Miliyan 50 kudin fansa, kafin sakin Direban.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,482 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!