Connect with us

Labarai

Ana fargabar rasuwar mutane 30 sakamakon kifewar Kwale-kwale a Neja

Published

on

Ana fargabar cewa, aƙalla mutane 30 sun rasu sakamakon kifewar wani kwale-kwale a ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Neja.

 

Rahotonni sun bayyana cewa, har zuwa fitar wannan rahoto ba a kai ga tabbatar da musababbin hatsarin ba, amma hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ta ƙaddamar da bincike kan lamarin.

 

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, Abdullahi Baba Ara, ya shaida wa BBC cewa, mutanen sun tashi ne daga garin Dugga domin zuwa ta’aziyya lokacin da hatsarn ya rutsa da su.

 

Baba Ara ya kara da cewa bayanan farko da suka samu sun nuna cewa wani kututture ne da ke cikin ruwan ya haddasa hatsarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!