Connect with us

Labarai

Ana fuskantar cizon maciji 43,000 duk shekara a Najeriya

Published

on

Binciken da Kungiyar Masanan Ilimin Guba ta Najeriya (Toxinological Society of Nigeria) ya gudanar ya nuna cewa Najeriya na samun kusan mutane 43,000 da macizai ke ciza a duk shekara, inda ake rasa rayukan kusan 1,900 sakamakon rashin isasshen maganin antivenom.

Rahoton ya kuma samu goyon bayan wani bincike daga kungiyar duniya ta Strike Out Snakebite Initiative, wadda ta bayyana cewa akalla kashi 50 cikin 100 na cibiyoyin lafiya a Najeriya ba su da cikakken ikon kula da masu cizon maciji. Kungiyar ta ce raunin tsarin lafiya, karancin kayan aiki da kuma wahalar samun antivenom na kara haddasa mutuwar da za a iya kauce wa.

Masana daga wadannan kungiyoyi sun bayyana cewa farashin antivenom na kai N180,000 zuwa N250,000 a kashi guda, lamarin da ya wuce karfin yawancin ‘yan kasa, musamman manoma da mazauna karkara. Sun bukaci Gwamnatin Tarayya da ta rage farashi ko ta samar da maganin kyauta, tare da bunkasa samar da shi a gida domin rage dogaro da shigo da shi daga kasashen waje.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!