Labarai
Ana gudanar da bincike kan asusun NNPCL- Wale Edun

Ministan Kudi da Tattalin Arziki na Najeriya Wale Edun, ya tabbatar da cewa, ana gudanar da bincike kan asusun kamfanin mai na NNPCL, domin inganta tsarin yadda kamfanin ke hada-hadar kudaden shigar sa.
Mninista Wale Edun, ya bayyana hakan ne a birnin Washington DC na Amurka, yayin da ya ke jawabi a taron zuba jari a Nijeriya da aka gudanar a kasar ta Amurka.
A cewar sa gwamnatin tarayya na kokarin daidaita asusun ajiyarta.
Haka kuma, ya ce, kamfanin NNPCL na sa ran zai samar da karin kudaden shiga na musayar kudin waje ga asusun gwamnati.
Wale Edun, ya kuma yi karin haske da cewa, ana gudanar da binciken kwakwaf ne ga NNPCL domin fahimtar yadda kamfanin ya yi hada-hadar kudade a baya kafin cire tallafin man fetur da kuma bayan cire tallafin.
You must be logged in to post a comment Login