Labaran Kano
Najeriya na fama da karancin maganin cutar Zubar Jini – Gidauniya
Wata gidauniya da ke rajin yaki da yaduwar cutar zubar jini da aka fi sani da Hemophilia wato Hemophilia Foundation of Nigeria, ta ce, rashin wayar da kan jama’a da Kuma karancin magungunan cutar na daga cikin manyan dalilan da ke yin zagon kasa ga yaki da cutar a kasar nan.
Shugabar gidauniyar ta Hemophilia Foundation of Nigeria, Mrs Meghan Doke Adodorin ce ta bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan yadda za a wayar da kan jama’a game da illar cutar da Kuma hanyoyin dakileta.
Ta ce, yawancin magungunan yaki da cutar da su ke bai wa masu fama da cutar, suna samo shine daga kungiyoyin ba da tallafi kan harkokin lafiya na kasashen ketare.
“Yawancin magungunan yaki da cutar na da tsada sosai, wanda masu fama da cutar marasa galihu ba za su iya saya ba” Inji Adedorin.
Dr Ibrahim Musa:Cutar rashin tsayawa jini na iya kisa farat daya
Ta kara da cewa, a wasu lokutan akan haifi yara da wannan lalura ta zubar jini amma iyayen su ba sa sanin hakan sai su zaci wata cuta ce ta daban wanda hakan ne ya sanya su ka ga dacewar gayyatar masu ruwa da tsaki domin nemo mafita kan yadda za a dakile yaduwar cutar da Kuma hanyoyin samar da maganin cikin sauki.