Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Zamu samar da magunguna da kayan gwaji a Kano – SACA

Published

on

Hukumar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta jihar Kano (SACA), ta ce, gwamnati za ta kara inganta asibitocin jiha tare da sanya kayan gwaji da magunguna ga masu fama da cutar hanta a wani mataki na dakile yaduwarta.

Shugaban hukumar Dakta Sabitu Yusha’u Sha’aibu Shanono ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na nan freedom rediyo a wani bangare na bikin ranar masu fama da ciwon hanta ta duniya da ke gudana a yau.

Ya kuma ce, sun wayar da kan mutane game da illar cutar hanta tare da shawartar mutane da su rika zuwa asibiti mafi kusa da su ana musu yi musu gwaji.

Ya kuma ce, masu juna biyu da jarirai cutar tafi baraza garesu, a don hakane ma hukumar ke ta kokarin wayar da kan jama’a don dakile ta

Dakta Sabitu Shanono ya kuma ce cutar tanada illa sosai tare da saurin kashe mutane duba da cewar ba ta nuna alamu da wuri.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!