Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Ana sa ran a kowanne lokaci hukumar INEC zata sanar da sakamakon zaben gwamnan na Jihar Kaduna

Published

on

Daga yanzu zuwa kowane lokaci ana saran hukumar zabe ta kasa INEC za ta sanar da sakamakon zaben Gwamnan jihar Kaduna da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

Rahotanni sun ce ana saran baturen zaben jihar Farfesa Muhammed Yahuza Bello zai sanar da sakamakon zaben bayan tattara dukkannin sakamakon kananan hukumomin jihar Ashirin da uku.

Haka zalika sakamakon da baturan zabukan kananan hukumomin suka gabatar ya nuna cewa gwamna Nasir Elrufai shike kan gaba inda ya samu nasara a kananan hukumoi goma sha hudu.

Kananan hukumomin da ya samu galaban lashe zabukansu sun hada da: Makarfi da Soba da Kudan da Ikara da Kauru da Kubau da Kaduna South da Giwa da kuma birnin Gwari.

Sauran sun hada da: Sabongari da Lere da Kaduna North da Zari’a da kuma Igabi.

Yayin da abokin fafatawar sa na jam’iyyar PDP Isa Ashiru na jam’iyyar PDP ya samu nasara a kananan hukumomi tara da suka hada da:

Jaba, da Kachia da Kaura da Kajuru da Zango Kataf da Sanga da Chikun da kuma Jema’a.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!