Connect with us

Kiwon Lafiya

Dubban jama’a a jihar Rivers sun gudanar da zanga-zanga bisa dakatar da tattara sakamakon zabe

Published

on

Dubban Jama’a a jihar Rivers sun gudanar da zanga-zangar adawa da matakin dakatar da tattara sakamakon zaben Gwamna da hukumar INEC ta yi wanda ke zuwa bayan rikice-rikice da zargin magudin zabe a wasu mazabun jihar.

Matakin dakatar da tattara sakamakon zaben ya zo ne bayan da a ranar Lahadi da ta gabata wasu gungun mutane sanye da kayan soji dauke da makamai suka yiwa cibiyar tattara sakamakon zaben jihar kawanya, tare da neman hukumar zabe INEC ta dakatar da aikinta, wanda kuma daga bisani rundunar sojin kasar ta ce ba jami’anta ba ne.

A jiya Litinin dai dubban magoya bayan jam’iyyar APC mara rinjaye a jihar tare da kungiyoyin fararen hula ne suka gudanar da zanga-zangar don adawa da matakin dakatar da zaben.

Tuni dai gwamnan jihar Nyesome Wike ya zargi hukumar INEC jami’an tsaro da kuma Jam’iyyar APC da yunkurin juya sakamakon zaben.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!