Labaran Kano
Ana tsaka da nada sabon sarkin Bichi
Nan gaba kadan ne za’a sanar da sabon sarkin Bichi bayan da gwamnatin Kano ta nada Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin sabon sarkin Kano.
A dazu ne dai Sarkin Bai da Makaman Kano da Madakin Kano da Sarkin Dawaki Mai tuta tuni sun hallara a fadar gwamnatin Kano yayin da suka nada Aminu Ado Bayero a matsayin sabon sarkin na 15 a daular Fulani.
Wakiliyar mu ta fadar Gwamnati Zara’u Nasir ta rawaito cewa, ta bayyana cewar a halin yanzu ana dakwan wanda zai gaji sarkin Bichi Aminu Ado Bayero a matsayin sarkin Bichi.
You must be logged in to post a comment Login