Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ana zanga-zanga a jihar Osun kan karin kudin wuta da man fetur

Published

on

Da sanyin safiyar yau Juma’a ne hadakar kungiyoyin kishin al’umma a garin Osogbo na jihar Osun suka fara gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna adawarsu ga Karin farashin man fetur da kuma kudin wutar lantarki.

Rahotonni sun bayyana cewa, an fara gudanar da zanga-zangar ne da misalign karfe 8:30 na safe a dandalin Freedom Park.

Masu zanga-zangar dai na dauke da kwalayen da ke dauke da kalaman nuna adawa da Karin kudin lantarki da kuma na man fetur wanda gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi.

Haka kuma masu zanga-zangar sun bukaci gwamnatin da ta janye Karin farashin don kuwa bai zo a lokacin da ya dace ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!