Connect with us

Labarai

Ana zargi alkali da baiwa ‘yan sanda satar amsa

Published

on

A kwanakin baya an samu labarin ‘yansanda da ake zargin sun daki wani matashi da dukan yayi sanadiyar rasa ransa, yayin da aka gurfanar da wadanda  ‘yan sanda da ake zargi a gaban kotu.

Daya daga cikin shakikin marigayin ya koka da cewa Alkalin dake gabatar da shari’ar mai suna Mannir Madugu na fadawa daya daga cikin ‘yan sandan da suka daki marigayin irin tambayar da zai amsa, hakan yasa yayi wa alkalin magana akan meyasa zai ke baiwa ‘yan sandan satar amsa sai wannan alkali yace masa ya barshi aikin sa yake yi dalilin da yasa yayi shiru.

An yi garkuwa da alkalin

Walter Onnoghen:ya kalubalanci rashin cancantar alkalin kotun da’ar ma’aikata

Rundunar sojin Najeriya ta yi holin mutane 13 da ake zargin su da hannu wajen bacewar Janar Idris Alkali

Ya kara da cewa abunda ya bashi haushi  da kuma takaici shine irin tambayar da wannan dan sanda yake masa na cewa wai shin marigayin yana da aljanu ne ko kuma wata cuta shi kuwa ya bashi amsa da cewa shi bai san wannan dan uwan na shi da wata cutar iska  ko wani abu makamancin haka.

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!