Connect with us

Labarai

Ana zargin makarantu masu zaman kan su da neman kudi

Published

on

Duba da muhimmancin ilimi a fadin kasar nan aka samar da makarantu  masu zaman kansu don cike gurbin gazzawar da makarantun gwamnati suka yi.

Sai dai abun ba haka yake ba a wannan lokaci kasancewar ana bude makarantun masu zaman kansu don neman kudi ga kuma rashin wadattun ajujuwa uwa uba kuma ga rashin bin ka’ida ba.

Tuni dai ake ta zargin cewa ana bude makarantun masu zaman kansu ne domin neman kudi.

Yawan bude makarantu marasa ajujuwa da yawa na nema zama ruwan dare a jihar nan, inda za a ga dakuna biyu ko daya ana mayar sa makarantun Nursery da firimare.

Al’ummar garin Kiru sun koka kan matsalar rashin asibitoci da makarantu

Za mu magance cunkoso a makarantu-KSSSMB

Gwamnatin Kano ta soke Makarantun ‘Yan Mari

Amma dai masu bude irin wannan makarantun basa la’akari da fili ko gurin da yara zasu yi wasa.

Akwai unguwani da suke da irin wannan makarantu a kano wanda suka hada da Rijiyar Zaki da Kurna da dai sauran su.

Akan hakan ne wakiliyar mu  Hafsat Abdullahi Danladi ta zanta da wasu iyaye kan ko suna la’akari da  girman muhallin makarantun da Suke sa ‘ya’yan su, yayin da wasu ke cewa akasari sun duba saukin kudin makaranta.

Haka kuma wasu ke ganin cewar ba girman muhalli ba ne karatu illa dai ‘ya’yan su za su sami ilimin zamani

A nasa shugaban hukumar masu kula da makarantu masu zaman kansu ta Jihar  Abba Dan kawu  ya bayyana irin ka’idojin da ya kamata a bi wajen bude makarantu masu zaman kansu.

Ya ce an fi so a sami filin wasa mai girma da kuma wadatattun azuzuwa da dalibai za su dauki darusa a ciki.

Maitamakiyar shugaban kungiyar masu zaman kansu ta kasa Hajiya Maryam Magaji ta ce, kamata gwamnati ta rufe duk irin wannan makarantu da aka ma ta bude basi ka’ida ba musman masu budewa a daki guda koh biyu.

Masana a harkokin ilimi sun yi kira ga masu iri wanann dabi’ar da su gujii bude irin wadanan  makarantun da ba bisa ka’ida ba.

Coronavirus

Masu Corona 759 ke jinya a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da kamuwar mutane 3 da cutar Covid-19 a jihar.

Ma’aikatar lafiya ta jihar ce ta sanar da hakan a shafinta na Twitter da misalin 11:29 na daren Alhamis.

Har ila yau, karin mutane 4 sun warke daga cutar kuma tuni aka sallame su a ranar Alhamis din.

Yazuwa yanzu mutane 939 ne aka tabbatar sun kamu da cutar Corona a jihar Kano, 139 daga ciki sun warke, sai mutane 41 da suka rigamu gidan gaskiya.

Ma’aikatar lafiya ta Kano ta ce yanzu haka masu dauke da cutar 759 ke cigaba da samun kulawar jami’an lafiya a cibiyoyin killace masu cutar dake nan Kano.

Continue Reading

Coronavirus

An samu raguwar masu cutar Corona a ranar Alhamis

Published

on

Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta sanar da samun sabbin masu dauke da cutar COVID-19, 182 a jihohi 15 na kasarnan da birnin tarayya Abuja.

Hukumar ta wallafa hakan ne a daren Alhamis ta shafinta na Twitter.

NCD ta kamar kullum jihar Legas ce ke kan gaba wajan adadin mafi yawa na wadanda suka kamu da cutar da mutane -111babban burinin tarayya Abuja ta samu mutane -16 jihar Akwa Ibom mutane-10, jihar Oyo mutane-8.

Jihohin Kaduna da Delta na da mutane 6-6 yayin da jihar Rivers keda mutane-5, jihohin Ogun da Ebonyi mutane 4-4 suka kamu jihar mutane Kano-3 jihohin Plateau da  Gombe da kuma Kwara mutane 2-2 suma jihohin Kebbi da   Bauchi da  Borno mutum 1-1.

Mutane 8,915 suka kamu da cutar a sassan kasar nan daban daban.

Daga ciki mutane 2,592 sai kuma mutane 259 da cutar ta hallaka.

Adadin mutum 182 da aka samu a ranar Alhamis shine adadi mafi karanci cikin kwanaki 12 da suka wuce inda a kullum ake samun masu dauke da cutar sama da 200 a kasar.

Continue Reading

Labarai

Tambuwal zai gana da Buhari kan harin ‘yan ta’adda a Sokoto

Published

on

Fadar shugaban kasa ta shirya ganawa tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da gwaman jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal kan kazamin harin da aka kai a daren ranar Laraba wanda ya shafi wadanda ba su ji ba ba su gani ba, a yankin kudu maso gabashin jihar ta Sokoto.

Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ne ya bayyan hakan ta cikin wata sanarwar da mai baiwa gwamnan shawara kan kafafan yada labarai Muhammad Bello ya sanya wa hannu.

Sanarwar tace gwamnan ya jajantawa al’ummar da harin ya shafa sannan gwaman ya baiwa hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA umarnin ta ziyarci wurin da aka kai harin domin tan-tance irin barnar da aka aikata da kumar samar da kayan jin kai ga mutanen da harin ya shafa.

Tambuwal ya shaidawa masu rike da masarautun gargajiya da masu ruwa da tsaki na yankin cewa bayan tattaunawa tsakanin jiya da yau da fadar shugaban kasa ya samu gayyata domin ganawa da shugaban kasa domin shawo kan alamarin.

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 324,753 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!