Connect with us

Labaran Kano

Hukumar alhazai ta Kano zata dauki mazauna Saudiya ma’aikatan wucin gadi

Published

on

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta ce daga yanzu zata dauki ma’aikatan da zasu gudanar da aikin hajji daga cikin mazaunan Saudiya ne da ta tantancesu tare da amincewa da su.

Idan za’a iya tunawa dai a cikin wani faifan bidiyo na wata mata da ma’aikatan hukumar mazauna Saudiya da ke nuni da wani jami’a wanda ake cewa center officer na karamar hukuma da ake zargin ya damfari  ta  kudin guziranta a lokacin aikin hajjin bara.

Ko da hukumar alhazai ta kafa kwamitin don binciken kan al’amari har kawo yanzu babu wani bayani, hasali ma tuni aka nemi ma’aikacin aka rasa.

Sakataren hukumar alhazai Alh Muhammad Abba Dambatta a wata sanarwa da ya fitar jiya ya bayyana cewar hakan ba zata sake faruwa tuni suka samar da mafuta  don magance afkuwan hakan.

Alhaji Dambatta ya ce hukumar zata kaddamar da wani asibiti na hukumar alhazan Kano karkashin kulawar hukumar alhazai ta ksa wato NAHCON.

Ya kara da cewa tana dab da fara dasa harshashen aikin gina wani gida  mai dauke da gadajen alhazai kimanin dubu 500 a nan Kano.

Da yake Magana shugaban hukumar Abdullahi Saleh Pakistan ya bukaci dukkanin jami’ai da su kasance masu tsoro wajen gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.

 

Coronavirus

Masu Corona 759 ke jinya a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da kamuwar mutane 3 da cutar Covid-19 a jihar.

Ma’aikatar lafiya ta jihar ce ta sanar da hakan a shafinta na Twitter da misalin 11:29 na daren Alhamis.

Har ila yau, karin mutane 4 sun warke daga cutar kuma tuni aka sallame su a ranar Alhamis din.

Yazuwa yanzu mutane 939 ne aka tabbatar sun kamu da cutar Corona a jihar Kano, 139 daga ciki sun warke, sai mutane 41 da suka rigamu gidan gaskiya.

Ma’aikatar lafiya ta Kano ta ce yanzu haka masu dauke da cutar 759 ke cigaba da samun kulawar jami’an lafiya a cibiyoyin killace masu cutar dake nan Kano.

Continue Reading

Labarai

Tallafa wa mabukata na kawo rahamar Ubangiji:   Dr Bashir Aliyu Umar

Published

on

Babban limamin masallacin Alfurkan dake Alu Avenue a karamar hukumar Nasarawa, Dakta Bashir Aliyu Umar, ya ja hankalin mawadata da su rika tallafawa raunana a cikin al’umma musamman ma a wannan lokaci da ake fama da matsin rayuwa sanadiyyar annobar Covid 19.

Dakta Aliyu Umar, ya bayyana hakan ne yayin rabon tallafin kudi da kayan situru da gidauniya tallafawa mabukata watau Ramadan Trust Initiative ta gudanar a masallacin na Alfurkan.

Limamin ya ce nuna jinkai ga juna a cikin al’umma na daga cikin abunda ke kawo saukar jinkan Allah ga al’umma.

A nasa bangaren mataimakin sakataren kungiyar Malam Umar Muhammad, cewa ya yi, sun raba tallafin ne ga mata domin su ja jari domin su dogara da kansu.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya rawaito cewa fiye da mabukata 50 ne suka amfana da tallafin.

Continue Reading

Coronavirus

Wadanda suka kamu da Corona sun kai 936 a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da samun karin mutane 13 dauke da cutar Covid-19 a jihar a ranar Laraba.

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ce ta sanar da hakan a shafinta na Twitter a daren Larabar da misalin karfe 11:45 na dare.

Ma’aikatar lafiyan ta Kano ta ce an sallami karin mutum guda wanda ya warke daga cutar a ranar Laraban, sannan karin mutum 3 cikin masu dauke da cutar sun rigamu gidan gaskiya.

Yazuwa yanzu adadin masu dauke da cutar a Kano sun kai 936.

Mutane 135 daga ciki an sallame su bayan da suka warke sarai daga cutar.
41 daga ciki kuma sun rigamu gidan gaskiya.

Yanzu haka dai masu fama da Corona 760 ne ke cigaba da samun kulawar jami’an lafiya a cibiyoyin killace masu dauke da cutar dake Kano.

A ranar Alhamis dinnan ne gwamnatin Kano tace zata shiga zagaye na biyu na rabon tallafin rage radadin dokar zama gida kan Corona ga mabukata.

Wakiliyar Freedom Radio a fadar gwamnatin Kano Zahra’u Nasir ta rawaito mana cewa a ranar Alhamis din ne ake sa ran gwamna Ganduje zai bude cibiyar daukar samfurin gwajin masu cutar Corona a unguwar Sabon Gari dake Kano.

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 324,753 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!