Connect with us

Labaran Kano

Za mu magance cunkoso a makarantu-KSSSMB

Published

on

Hukumar da ke kula da manyan makarantun sakandire ta jihar Kano ta ce ta  shirya tsaf domin magance matsalar samun cunkoso a ajujuwan da ke makarantun jihar ta hanyar gina bennayi da zasu samar da sababbin ajujuwa ga dalibai.

Babban sakatare a hukumar Dr Bello Shehu ne ya bayyana hakan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio da ya mayar da hankali kan magance matsalolin manyan makarantun sakadiren kasar nan.

Ya kara da cewa, a kullum hukumar na gudanar da kewaye a makarantun sakandire wanda hakan ne ya basu damar gano malamai masu aikata laifukan da suka shafi tauye hakkin koyarwa kuma za su dauki matakin da ya dace akansu.

Sai dai ya ce hukumar ta shirya domin baiwa malamai damar zuwa karo karatu matukar abinda malamin zai koyo yana kan fanni da yake koyarwa a wani mataki na samar da ingantaccen karatu ga dalibai.

Dr Bello Shehu ya kuma ja hankalin shugabannin makarantu da su kiyaye bayar da damar yin amfani da makarantun matukar ba sha’anin da ya shafi harkar koyo da koyarwa ba.

Labaran Kano

Al’umma na da damar yin kiranye ga wakilan su- Barista Turmuzi

Published

on

Wani lauya a nan kano, Barista Sale Muhammad Turmuzi, ya ce, jama’a suna da ‘yancin yin kiranye ga wakilansu da ke jiran hukuncin kotu, bayan daukara kara a kotu ta gaba, bisa wani zargin cin hanci da rashawa.

Barista Sale Muhammad Turmuzi, ya bayyana hakan ne ta shirin Muleka mu gano na musamman na nan tashar freedom Rediyo da ya gudana a daren jiya.

Batista Sale Turmuzi, ya kara da cewa, a tsarin yadda doka ta tanada, duk wani dan majalisa da ya rasa kaso daya bisa uku na zaman majalisa zai iya rasa kujerarsa matukar bashida kwararan hujjoji.

A daina siyasar uban gida a Najeriya domin cigaban demokradiyya -Farfesa Kamilu

Shugaba Buhari yayi ganawar sirri da wasu tawagar yan siyasa daga Kano

Sale Muhammad Turmuzi, ya kuma ce, an samu gagarumin ci gaba a bangaren yaki da cin hanci da rashawa a fadin kasar nan musamman a bangaren shari’a, bisa yadda ake ganin Kotuna a wannan lokaci suna yanke hukuncin da ke turawa da masu rike da mukaman siyasa zuwa gidan gyaran hali.

Muhammad Sale Turmuzi, ya kuma nanata cewa, zartas da hukuncin zaman gidan gyaran hali kan tsoffin gwamnoni kuma sanatoci masu ci kan cin hanci zai taimaka gaya wajen karfafa mulkin dimukuradiyya.

Continue Reading

Labaran Kano

Gwmnatin Kano ta ankarar da masu saida magugunan dabbobi

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci masu sana’ar sayar da magungunan dabbobi ta jiha da su maida hankali wajen gudanar da kasuwancin su bisa doka da oda.

Babban sakataren ma’aikatar gona na jihar Kano Alhaji Adamu Abdu Faragai ne ya ja hankalin ‘yan kungiyar masu sayar da magungunan dabbobi na jiha, yayin wata ziyara da suka kawo masa ziyara ofishinsa.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran ma’aikatar gona, Hafizu Lawan ya sanyawa hannu.

Alhaji Adamu Abdu Faragai ya ce bin doka da oda na daga cikin hanyoyin da za su basu damar gudanar da kasuwancin su cikin walwala da kuma kawo ingantuwar tattalin arziki.

Hukumomin kiwon lafiya na yin dukkanin mai yuwa kan cutar lassa- Sarkin Kano

Kano: Hukumar KAROTA ta kai sumame wajen boye magunguna

Wasu magungunan kwari da manoma ke amfani da su na da illa ga lafiyar dan Adam

Babban sakataren ma’aikatar gona ya bayyana goyon bayan ma’aikatar wajen kawo ci gaba a tsarin kasuwancin su don bunkasar tattalin arziki.

Da yake bayani, jagoran ‘yan kasuwar da suka kawo ziyarar Alhaji Garba Abdullahi Dawakin Kudu yace makasudin ziyarar ta su shine don neman goyon ma’aikatar tare da gabatar da kasuwancin su cikin ka’idar doka da hukumomin suka shimfida.

Alhaji Garba Abdullahi Dawakin Kudu ya kuma nemi ma’aikatar gona ta jihar Kano da ta tallafa musu wajen ganin kasuwancinsu ya bunkasa.

Continue Reading

Labaran Kano

BUK ta horas da mutane kan yadda zasu rika sarrafa kudaden su

Published

on

Cibiyar nazarin harkokin bankuna da kudi a musulince ta jami’ar Bayero, ta ce da yawa daga cikin kudaden da mutane suke kashewa a wannan lokacin suna kashesu ne ta hanyar da bata daceba.

Daraktan cibiyar Farfesa Binta Tijjani Jibril ce ta bayyana hakan yayin taron horar da Ilimin harkokin kudi ga kungiyoyin makarantun addinin Musulunci da cibiyar ta gudanar yau a tsangayar koyar da ilimin shari’a dake jami’ar ta Bayero a nan Kano.

Farfesa Binta Tijjani Jibril ta kuma ce ya kamata mutane su koyi yadda za su dinga kashe kudaden su ta hanyar da ta dace ta yadda tattalin arzikin kasar nan zai bunkasa yadda ya kamata a hanyoyi da dama.

Ta kuma ce da yawa daga cikin mutanen kasar nan suna samun kudade a ayyukan da suke gudanarwa sai dai basu san irin hanyoyin da za su bi ba wajen kashe kudaden na su ta hanyar data dace.

Farfesa Binta Tijjani Jibril

Farfesa Binta ta kuma yi kira ga gwamnatocin kasar nan kan su dage wajen bunkasa ilimi a tsakanin al’umma ta yadda za su iya kashe kudaden su ta hanyar da ta dace.

Har ila yau ta kuma ja hankalin gwamnati wajen samar da ayyukan yi tsakanin al’ummar kasar nan, ta yadda za’a rage mutanen da basu da ayyukan yi.

Wasu daga cikin mutanan da suka halarci taron horarwar sun bayyana jindadin su, bisa yadda aka gudanar da laccar musamman yadda aka nuna musu yadda za su kashe kudaden su a tsarin addinin musulinci.

Masana harkokin kudi da dama ne suka halarci taron horarwar inda sukayi bayanai da dama kan yadda ya kamata mutune subi wajen kashe kudaden su.

Labarai masu alaka:

BUK: dalibai 300 sun sami tallafin karatu

Jami’ar Bayero ta bukaci mahukunta su cigaba da amfani da takardun SUKUK don ciyar da al’umma gaba

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!