Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Anyi kira ga shugaba Buhari da ya kawo karshen matsalar tsaro

Published

on

Kungiyar Inuwar Musulman Najeriya wato Islamic Forum of Nigeria, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari daya rubanya kokarinsa wajen kawo karshen matsalar  tsaro dake addabar yankin Arewacin kasar nan.

Mai binciken kudin kungiyar ta kasa Malam Sale Adamu Kwaru, ne bayyana hakan a  taron kungiyar na shekara-shekara da ya saba  gudana, wanda akayi a nan Kano.

Malam Sale Kwaru, ya ce ba yadda za samu cigaba mai dorewa matukar babu ingantaccen zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’ummar kasar nan.

Labarai masu alaka.

Kyautatawa malamai ya zama wajibi- Shekarau

Mahukunta su mai da hankali kan al’umma -Limami

Ya kuma ce jihohin Arewacin kasar suyi koyi da  takwarorin su na  kudanci wajen aiyyukan cigaba, tare da samar da tsayayyun manufofi .

Taron ya samu halartar malamai daga sassan kudancin kasar nan da sauran gurare suka halarci taron domin lalubo bakin zare kan matsalolin tsaro dake damun kasar nan, kamar yadda wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa, ya ruwaito mana.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!