Labarai
APC ce za ta lashe zaɓen ƙananan hukumomi baki ɗaya – Ganduje
Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce, In Allah ya yarda jam’iyyar APC ce za ta cinye zaɓen baki ɗaya.
Ganduje ya bayyana hakan ne, jim kaɗan bayan da ya kaɗa ƙuri’arsa a mazaɓarsa.
A cewar sa, la’akari da yawan fitowar jama’a na nufin jam’iyya mai mulki zata lashe dukkan kujerun.
Ganduje ya kuma ce, an gudanar da zaɓen cikin tsari me kyau.
Zuwa yanzu dai an fara tattara sakamakon zaɓe a wasu mazaɓun bayan da aka kammala kaɗa ƙuri’a.
You must be logged in to post a comment Login