Connect with us

Labaran Wasanni

Arsenal: Aubameyang ya tsawaita kwantiragin sa da kungiyar

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang, ya rattaba hannu a yarjejeniyar ci gaba da zama kungiyar har tsawon shekaru uku masu zuwa.

Kwantiragin dan wasan mai shekaru 31 da kungiyar zai kare a karshen wannan kakar wasannin da muke ciki.

Tun dai a lokacin da Aubameyang da dawo kungiyar ta Arsenal daga Borussia Dortmund a watan Janairun shekarar 2018, ya yi nasarar jefa kwallaye 55 a wasanni 86.

Aubameyang dai ya kawo karshen jita-jitar barin sa kungiyar, da ya amince da sabon kwantiragin na karin shekaru uku da kungiyar ta Arsenal.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 331,771 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!