Connect with us

Labarai

Artabu: Ƴan Bijilante sun cafke masu garkuwa da mutane a Kano

Published

on

Jami’an tsaron suntirin Bijilante na jihar Kano, sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da yin garkuwa da mutane a karamar hukumar Sumaila.

Shugagaban ‘yan sintirin Bijilante na jihar Kano, Muhammad Kabir Alhaji ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai da yammacin jiya Litinin.

Ya ce mutanen biyu da suka kamo sun hadar da Ibrahim Gamji dan asalin kauyen Gomo da Tukur Ali dan asalin kauyen Kauyen Masu.

Muhammad Kabir ya ce, sun cafke wadanda ake zargin ne kwanaki kadan bayan da suka fafata da su, sannan suka kubutar da wasu da suka yi garkuwa da su, daga nan ne kuma jami’an suka ci gaba da bin sahun su ta hanyar bayanan sirri da suke samu har suka kame su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,482 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!