Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Arzikin ƙasa: Gwamnatin tarayya da jihohi sun raba sama da biliyan dari bakwai

Published

on

Hukumar kula da rabon arzikin kasa ta ce gwamnatin tarayya da Jihohi da kuma kananan hukumomi sun raba kudi naira biliyan dari bakwai na watan Satumba.

 

Gwamnatin tarayya ta karbi sama da naira biliyan dari biyu da saba’in da shida, inda jihohi suka karbi kusan naira biliyan dari da talatin da tara.

 

ƙananan hukumomi sun karbi naira biliyan dari da bakwai, da miliyan dari tara da talatin.

 

Jimillar kudin ya kai biliyan dari bakwai da talatin da tara da miliyan dari tara da sittin da biyar, na kudaden shiga da aka tattara a cikin watan Satumban jiya.

 

Wannan na cikin sanarwar bayan taro da hukumar ta fitar bayan ganawar da ta gudanar ta intanet, game da kudaden da aka raba a cikin wannan wata na Octoba da muke ciki.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!