Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Ashirye nake in sauka daga karagar mulki matukar hakan zai samar da zaman lafiya – Matawalle

Published

on

 

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce, a shirye yake da ya ajiye mukamin sa na gwamna matukar hakan zai sa a samu zaman lafiya a fadin jihar.

A cewar sa in har hakan ne mafita zai sa a samu saukin hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane to a shirye yak e ya sauka daga karagar mulkin jihar.

Matawalle, ya bayyana hakan ne ta cikin shirin siyasa a yau, na tashar talabijin din Channels wanda ya mai da hankali kan harkokin tsaro da ya shafi jihar musamman ma sanya dokar hana shawagin jiragen sama a sararin samaniyar jihar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a baya bayan nan.

‘‘Matukar sauka ta daga mulki za ta sa a samu zaman lafiya, tare da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jiha ta, ba tare da zubar da jinin su ba, a shirye nake da in sauka ko yanzu’’ a cewar Matawalle.

Gwamna Matawalle, ya kuma kara da cewa gwamnatin sa na nan akan bakarta na ci gaba da tattunawar sulhu da ‘yan bindiga don ganin an kawo karshen matsalolin tsaro da ke addabar jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!