Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Boko Haram: Sojoji 101 sun tsere daga bakin daga

Published

on

Rundunar sojojin kasar nan ta tabbatar da cewa wasu sojojinta guda dari da daya sun tsere daga bakin daga.

A cewar rundunar sojin wadanda aka nemesu aka rasa sun hada da masu mukamin manjo guda uku, kyaftin guda uku, laftanal guda shida da masu mukamin saja guda uku sai kuma sauran sojoji guda tamanin da tara.

A cewar ta sojojin sun tsere ne daga bakin daga bayan gumurzun da aka yi a garuruwan Marte da kuma Dikwa.

Jaridar Daily Trust, ta ruwaito cewa a wata takarda da ta samu mai kwanan wata daya ga watan Maris daga shalkwatar rundunar dakarun Operation Lafiya Dole, a birnin Maiduguri ta tabbatar da cewar sojojin sun gudu ne daga bakin aiki.

Takardar mai dauke da sa hannun Kanal A.O. Odubiyi, ta bukaci rundunar da ta saka sunayen sojojin a matsayin wadanda suka gudu daga bakin aiki, tare da bukatar samar da sabbin sojojin da zasu maye gurbin su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!