Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Ashleigh Bartey tayi ritaya daga fagen Tennis

Published

on

‘Yar wasa lamba daya ta duniya, Ashleigh Bartey ta ce tayi ritaya daga buga wasan kwallon Tennis.

Bartey ta bayyana haka ne kwatsam ba tare da tsammani ba, a ranar Laraba 23 ga watan Maris din 2022 a wani faifan Bidiyo da ta fitar ta na bankwana da magoya bayanta.

Cikin alhini gami da zubar da hawaye tace ”Abu ne mai wahala na iya cewa nayi ritaya, sai dai ina matukar farin ciki na kuma shirya da hakan.”

‘Yar wasan mai shekaru 25, ta bayyana aniyarta ta ajiye raket din nata makonni kadan bayan da ta lashe gasar Australian Open, kuma watanni shida bayan da tayi nasara a gasar Wimbledon ta shekarar da ta gabata ta 2021.

Zakarar gasar Grand Slam har karo uku ta kasar Australia, ta dai lashe kyautar lamba daya ta duniya a wasan Tennis a ranar 24 ga watan Janairun shekarar 2014.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!