Labarai
ASUP:ta yi barazanar tafiya yajin aikin gargadi na mako guda
Kungiyar malaman kwalejojin fasaha da kimiyya ta kasa ASUP tayi barazanar tafiyar yajin aikin gargadi na mako guda, sakamakon abinda ta kira na gaza biya mata bukatun ta da gwamnatin tarayya tayi, duk da cewa sun cimma yarjejeniyar hakan tun farko.
Sakataren yadda labaran kungiyar ta ASUP na kasa Mista Chris Nkoro ne ya bayyana matakin kungiyar, lokacin da yake jawabi yayin taron majalisar zartaswar kungiyar ta kasa karo na casa’in da hudu wanda ya gudana a garin Kaduna.
Idan za’a iya tunawa a farkon watan Fabrairun bana ne kungiyar ta janye yajin aikin watanni biyu da ta tsunduma biyo bayan da ta cimma yarjejeniyar da gwamnatin tarayya.
Rahotanni sun nuna cewa Mista Chris Nkoro bai bayyana hakikanin lokacin da kungiyar zata tsunduma yajin aikin na kwanaki bakwai ba, sai dai yace nan bada jimawa zasu sake komawa yajin aikin.
Kungiyar ta zargi gwamnatin tarayya da yin biris da tarjejeniya da suka kulla kafin janye yajin aikin da ta tsunduma a watan Fabrairun bana, tare da cewa hakan na daga cikin abinda yake ciwa mabobin ta tuwo a kwarya.
Majalisar zartaswar kungiyar ta kasa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta fara nazarin kan tattaunawar da suka yi a baya da kuma yarjejeniyar da suka kulla ba tare da bata lokacin ba, tare da cewa matsawar ta gaza hakan shakka babu nan gaba kadan zata tsunduma yajin aikin na gargadin.