Connect with us

Labarai

ASUU na shirin tsunduma yajin aikin sai Baba ta gani

Published

on

Ƙungiyar Malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU shiyyar Kano, ta sha alwashin tsunduma yajin aikin sai Baba ta gani nan da mako guda matuƙar gwamnatin tarayya ba ta cika mata alƙawuran da ta dauka dangane da yarjejeniyar da suka ƙulla ba.

Kwamared Abdulkadir Muhammad shugaban ƙungiyar wadda ta ƙunshi mambobinta na Jami’ar Bayero da ta Northwest da Jami’ar jihar Kaduna ta Aliko Dangote da ke Wudil da ta Sule Lamido da ke Kafin Hausa da ABU Zaria da jami’ar Gwamnatin tarayya da ke Dutse, ya bayyana hakan ne a yau Litinin yayin taron manema labarai da suka gudanar.

Ya ce, sun dauki wannan mataki ne sakamakon zaman da suka yi a ranakun 8 da kuma 9 ga watan nan da muke ciki na Nuwamba a jami’ar jihar Taraba, biyo bayan janye yajin aikin gargaɗi da suka shiga a baya na tsawon makonni 2.

Kwamared Abdulkadir Muhammad, ya kuma bayyana cewa, zuwa yau da suka gudanar da wannan taron manema labarai, rahoton da suka samu daga uwar ƙungiyar ta ƙasa sun bayyana cewa babu wani yunƙuri da gwamnatin tarayya ta yi na cika alƙawuran da ta yi musu.

Ya kuma ce, “Don haka da zarar lokacin da muka ɗiba ya ƙare ba tare da gwamnati ta cika wannan alƙawari ba za mu zauna tare da sanar da matakin da za su ɗauka na gaba.”

Da ya ke amsa tambaya kan batun matakin gwamnatin tarayya na babu aiki babu albashi da gwamnatin ta ɗauka a kansu a yajin aikinsu na baya, shugaban shiyyar Kano na ƙungiyar Malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU Kwamared Abdulkadir Muhammad, ya ce, ” Mu ma muna da irin wannan tsari, kuma ba ma tsoronsa ko a baya da gwamnatin ta fito da wannan tsarin zalunci sai da muka shafe watanni 8 muna yajin aiki ba tare da gajiyawa ba.”

“Babban burinmu shi ne gwamnatin tarayya ta yi abinda ya dace, duk gwagwarmayar da muke yi muna yinta ne a kan neman gwamnati ta magance matsalolin da jami’o’i ke fuskanta da kuma namu matsalolin, amma su burinsu shi ne su kashe makarantun gwamnati saboda yadda ƴan siyasa suka mayar da samar da irin waɗannan makarantu tamkar ayyukan mazaɓu.”

” Saboda haka ba za mu daina gwagwarmaya ba lallai har sai gwamnati ta gyara wadannan matsaloli, saboda idan kuka duba duk yawanci zaƙaƙuran ɗaliban  ƙasar nan a irin wannan jamio’i ake yaye su,” in ji Kwamared Abdulkadir Muhammad.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!