ilimi
ASUU ta koka kan jinkirin naɗa shugaban Jami’ar Northwest

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa ASUU, reshen Jami’ar Northwest da ke nan Kano, ta bayyana damuwarta kan jinkirin da aka samu wajen samar da sabon Shugaban jami’ar watau Vice Chancellor na dindindin.
ASUU, ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a Litinin ɗin makon nan mai ɗauke da sa hannun shugabanta na reshen jami’ar ta Northwest Kwamared Mansur Sa’id, da Sakatarenta Kwamared Yusuf Ahmad Gwarzo, inda ta bayyana cewa wannan jinkiri ka iya haifar da matsaloli wajen gudanar da harkokin jami’ar.
Haka kuma ta cikin sanarwar, Kungiyar ta ce wa’adin tsohon shugaban Jami’ar ya ƙare ne a ranar 15 ga watan nan da muke ciki na Oktoban bana, kuma tun daga lokacin Mataimakin Shugaban Jami’ar mai kula da Harkokin Karatu ne ke rike da mukamin shugaban rikon kwarya, inda ASUU ta ce wannan tsarin ba ya cikin dokar kafa Jami’ar Northwest ta shekarar 2012 wadda aka yi wa kwaskwarima.
ASUU ta jaddada cewa, bisa tanadin sashen 9 (2) na dokar jami’ar, nadin Shugaban Jami’a ya rataya ne a kan Hukumar Gudanarwa tare da tabbatarwa daga Mai Ziyarar Jami’ar, tare da cewa, dokar ta fayyace yadda za a gudanar da aikin tantancewa da nada wanda zai rike mukamin, wanda ya haɗa da ayyana kujerar a matsayin wadda babu mai ita, sannan a kafa kwamitin bincike da kuma miƙa sunan mutane 3 da aka zaba zuwa ga Majalisar gudanarwa domin tabbatar da guda daga cikinsu.
Kungiyar ta ce tana bibiyar lamuran da suka shafi nadin, inda ta tabbatar cewa Hukumar Gudanarwa ta kammala aikin ta har zuwa matakin zaben wanda ya dace da mukamin, a taro na musamman da aka gudanar ranar 2 ga Oktoba, 2025.
Sai dai ASUU ta nuna rashin jin daɗinta kan yadda Hukumar ba ta sanar da sakamakon taron ga ma’aikatan jami’ar ba, kuma ba ta miƙa sunan wanda aka zaɓa domin tabbatarwa ba.
ASUU ta yi gargadin cewa jinkirin ya na iya zama saba wa doka, tana kuma kira da a gaggauta ɗaukar mataki domin kauce wa haifar da tsaiko a harkokin gudanarwa da tsarin shugabanci.
Kungiyar ta kuma bukaci a bi ƙa’idar da doka ta tanada, ba tare da tsoma baki daga kowanne ɓangare ba.
A cewar ASUU shiyyar ta jami’ar Northwest, jinkirin tabbatar da sabon shugaban jami’ar na iya haifar da rashin tabbas a shugabanci da kuma tasiri ga ci gaban karatu da gudanarwa.
Kungiyar ta tabbatar da aniyar ta na kare mutuncin tsarin jami’o’i tare da tabbatar da bin ƙa’ida da gaskiya a duk harkokin gudanarwa na jami’ar.
You must be logged in to post a comment Login