Labarai
ASUU ta yi watsi da rancen kudi da gwamnatin tarayya za ta bai wa mambobinta

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU, ta yi watsi da shirin gwamnatin tarayya na bai wa malaman jami’o’i rancen kuɗi, tare da buƙatar gwamnatin da ta mutunta tare da sanya hannu da kuma aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma tun shekarar 2009.
Shugaban ƙungiyar ta ASUU shiyyar Kano Kwamared Abdulkadir Muhammad, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da kungiyar ta gudanar yau Alhamis.
Kwamared Abdulkadir Muhammad, ya bayyana cewa, ya kamata gwamnatin tarayya ta hana samar da jami’o’i masu zaman kansu kamar yadda ta sanar a baya ba wai iya na gwamnati kaɗai ba.
Shiyyar Kano na ƙungiyar ta ASUU da suka ƙunshi jami’o’in ABU Zaria da BUK da jami’ar jihar Kaduna KASU da KUST Wudil FUD da North West Kano da Kuma ta Sule Lamido da ke Kafin Hausa, sun cimma wannan matsaya ne yayin taron da suka gudanar.
Haka kuma ƙungiyar ta koka kan yadda malaman jami’o’i suka shafe shekaru 16 a kan albashi guda duk kuwa da cewa an samu tashin farashin Dala da hauhawar farashin kayayyakin amfanin yau da kullum da kuma tsawwala farashin Man Fetur.
Ta cikin takardar da shugaban na shiyyar Kano Kwamared Abdulkadir Muhammad ya karanta mai dauke da sa hannunsa, ƙungiyar ta kuma zargi gwamnatin tarayya da yunƙurin kassara jami’o’i mallakin gwamnati bisa rashin sanya kuɗaɗen da suka dace wajen tafiyar da harkokin koyo da koyarwa da harkokin gudanar da jami’o’i.
You must be logged in to post a comment Login