Labarai
Atiku na daga cikin waɗanda suka haddasa mana rigingimu- PDP

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ta yi iƙirarin cewa dan takararta na shugaban kasa a zaben da ya gabata na shekarar 2019 Atiku Abubakar na daga cikin waɗanda suka haddasa rigingimun da suka daɗe suna addabar jam’iyyar tare da cewa, ficewarsa ba za ta haifar da giɓi ba.
Mataimakin sakataren jam’iyyar kan harkokin yada labarai Ibrahim Abdullahi, ne ya bayyana hakan inda ya yi iƙirarin cewa Atiku na ɗaya daga cikin waɗanda ke hadassa fitina a cikin jam’iyyar.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ɗauki matakin ficewa daga PDPn ne a daidai lokacin da ya shiga wata haɗakar da ta haɗa jam’iyyun adawa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADC, a wani abin da ya ambata da shirin tunkarar babban zaɓen 2027.
Tun farko Atiku Abubakar ya sanar cewa ya raba gari da jam’iyyar ta PDP inda ya ce ya yi hakan ne bisa la’akari da yadda ta sauka daga tsarin da aka kafa jam’iyyar.
Malam Abdallahi ya ce ficewar Atiku ta nuna ba zai iya samar da adalci ba ko da ya samu mulkin Najeriya duba ya abinda ya ayyana da rarraba kawunan jama’a.
You must be logged in to post a comment Login