Labarai
Atiku ya kalubalanci matsayar gwamnonin PDP

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya kalubalanci matsayar gwamnonin jam’iyyar PDP wadanda suka nesanta jam’iyyar daga kawancen da Atikun ke yi.
A ranar Litinin ne kungiyar gwamnonin jam’iyyar ta PDP karkashin jagorancin gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed, suka bayyana cewa jam’iyyar ba za ta shiga cikin wata hadaka da kowace jam’iyya ba.
Sai dai a martanin da ya mayar, Atiku Abubakar ta hannun mataimakinsa kan yaɗa labarai Paul Ibe, ya jaddada bukatar fadada tattaunawar domin samun matsaya.
You must be logged in to post a comment Login