Connect with us

Labarai

Atiku ya bukaci a bai wa yan Najeriya damar zaɓar shugaban INEC da kwamishinoninta

Published

on

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa,Alhaji Atiku Abubakar, ya nemi a bai wa ‘yan Najeriya damar zaɓen shugaban hukumar INEC da kwamishinoninta kai tsaye.

 

Ya ce hakan zai taimaka wajen dawo da sahihancin zaɓe, ganin cewa zaɓen 2023 da ya gabata ya samu mafi ƙarancin halartar jama’a zuwa runfunan zabe.

 

Atiku ya kuma bukaci a sanya dokar da za ta tilasta amfani da katin BVAS da kuma tura sakamakon zaɓe ta kafar intanet, domin kaucewa rashin gaskiya da dogaro da kotu.

 

Ya ja hankalin cewa, idan ba a yi waɗannan gyare-gyaren ba, za a ci gaba da ganin jama’a na ƙin fita kada kuri’a, abin da zai barazana ga dimokuraɗiyya a ƙasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!