Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Atiku ya musanta ya karbi allurar riga kafin Korona

Published

on

Mataimakin darakatan yada labarai na tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, Muhammad Sunusi Hassan ya musanta rade-radin da ake yadawa  cewa an yi wa Atiku Abubakar riga kafin allurarar Corona.
 
Muhammad Sunusi Hassan ya ce hotunan da ake yadawa ba wasu hotuna ba ne illa wani tsofafin hotuna da a wani lokaci Alhaji Atiku Abubakar ya je asibiti a Dubai don duba lafiyar sa.
Akan haka ne mataimakin darakatan yada labaran ya nemi jama’a da su yi watsi da wannan batun.
Tun da fari dai a jiya Laraba ne daya daga cikin hadaman tsohon mataimakin shugaban kasa na kafafan sada zumunta ya wallafa a shafin sa na Twitter cewa Atiku Abubakar ya karbi riga kafin allurar Corona.
Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!