Siyasa
Ayyuka na gari yasa daruruwan ‘ya’yan Jam’iyyar APC sauya sheka zuwa NNPP a Doguwa – Hon. Abdurrashid

Shugabanci na gari da samar da ci gaban da ya kamata a karamar hukumar Doguwa ya sanya yayan Jam’iyyar APC daga sassanta daban daban ke ficewa daga Jam’iyyar zuwa NNPP Kwankwasiyya.
Hakan na da alaka da jagoranci na gari da shugaban karamar hukumar Hon. Abdurrashid Rilwan Doguwa ke gabatarwa.
A farkon watan da muke ciki na Maris ya karbi daruruwan Yayan Jam’iyyar ta APC Maza da Mata da suka dawo Jam’iyyar ta NNPP.
A cewarsu yadda yake gudanar da shugabanci ne ya ja hankalin su shigowa kuma za su kara janyo dubban mutane da basa Jam’iyyar zuwa cikinta.
Sun kuma ce sabo da sauraren su da akeyi Kuma ake kyauta ta musu da tallafi, da kuma gudunmawar kudin siyen filin makabartu da ya basu da yin gyare-gyaren masallatai da dai sauransu suma sunja hankalin su.
Hon. Abdurrashid Rilwan Doguwa dai tun daga hawansa shugabancin karamar hukumar ya samar da Azuzuwa a makarantu da dama da gyaran hanyoyi da inganta Noma da kiwo da samar da ruwan sha da dai sauran ayyukan More Rayuwa.
You must be logged in to post a comment Login