Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ayyukan da Ganduje ya kaddamar Jim kadan kafin ya bar karagar mulki

Published

on

Yayin da ya rage awanni wa’adin zagon karshe na biyu ya karewa Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kashe fiye da Biliyan bakwai wajen Gina gadar sama daga kofar mata zuwa Kwari tare da sa mata sunan sabon shugaban Kasa Bola Ahmad Tunubu.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan lokacin da yake bude gadar da Yammacin yau Lahadi.

Ganduje ya kuma Kara da cewar ‘Samar da gadar zai taimaka wajen saukaka zirga-zirga tare da bunkasa Kasuwanci da akeyi a wannan yakin’.

Wanda ya ce ‘an samar da gadar ne duba da irin cunkoso. da ake samu a hanyar sakamakon kasuwanni dake wurin’.

Haka zalika Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya kuma bude sabon ofishin hukumar zakka da Hubusi ta jihar Kano ta din-din-din tare da umartar Ma’aikatan hukumar musamman malamai, Yana Mai Kira ga ma’aikatan wannan hukumar da su dage wajen wayar da Kan mazauna karkara da masu kudi Muhimmancin bayar da zakka.

Freedom Radio ta ya ruwaito cewa Gwamna Ganduje ya kuma bude Asibiti a karamar hukumar warawa da wasu tituna a Unguwar Sabon Gari cikin karamar hukumar Fagge, Sai kuma ofisoshin Asusun tallafawa kananan Yara na Majalisar Dinkin duniya, da shagunan da gwamnatin ta gina a Ofishin kungiyar yan jaridu ta Kasa reshen jihar Kano dake Unguwar Farm centre.
Haka zalika ya samu nasarar bude wasu ayyuka a garin Ganduje dake Karamar hukumar Dawakin Tofa wanda su ne bude ayyukan sa na karshe a matsayin Gwamnan jihar Kano tsahon shekaru Takwas.

Rahoton: Abba Isa Muhammad

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!