Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Azal: Amarya ta kwarawa uwar gida tafasasshen ruwa a Kano

Published

on

Wata mata ta kwarawa kishiyar ta tafasasshen a jiki.

Hafsah Isa mai shekaru 21 wadda kuma ita ce amarya a gidan ta kwarawa kishiyar ta Daharatu Hamza mai shekara 21 ruwan zafin ne saboda saɓanin da suka samu.

Lamarin dai ya faru da safiyar ranar Laraba a unguwar Gayawa da ke ƙaramar hukumar Ungoggo anan Kano.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama wadda ake zargi bayan ƙorafin da ta samu.

Mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai da yammacin Laraba.

Kiyawa ya ce “A binciken da muka yi mun gano cewa rikici ne ya faru a tsakanin uwar gida Daharatu da kuma kishiyarta Hafsat lamarin da ya kai su ga hawa dokin zuciya”.

Sai dai ya ce, tuni aka miƙa Hafsah sashin binciken manyan laifukan don faɗaɗa bincike tare da ɗaukan mataki na gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!