Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Azal: Wani almajiri ya hallaka abokinsa a Kano

Published

on

A na zargin wani matashi da hallaka abokin sa a unguwar sheka gidan leda a karamnar hukumar Kumbotso.
Lamarin dai ya faru ne a yammacin jiya Laraba yayin da wasu matasa biyu da suka hadar da Shu’aibu da Abdullahi da ke wasan guje-guje inda Shu’aibun ke rike da almakashi kuma bayyi aune ba ya cakawa Abdullahi a kirji wanda yayi sanadiyyar mutuwarsa nan take.
Jami’in hurda da jama’a na rundunar yan sandan Kano ya tabbatar wa da Freedom Radio faruwar lamarin, inda ya ce suna ci gaba da tattara bayanai a kai, domin daukar matakin da ya dace.
A kwanakin nan dai ana samun yawaitar kasha-kashen mutane, a nan Kano, wanda kuma jami’an tsaro ke cewa suna iya bakin kokarin su wajen dakile hakan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!