Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

AZUMI: ‘Yan kasuwar Hadaddiyar Daular Larabawa sun rage farashi da kashi 75

Published

on

’Yan kasuwa a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa za su rage farashin kayayyakin su daga kashi 25 zuwa 75 cikin dari a lokacin watan Azumi na Ramadan  na bana.

 

Farashin da ’yan kasuwar za su rage zai shafi akalla nau’ika 30,000 na kayayyakin abinci da ake sayarwa a kasar.

 

Kamfanin Dillancin Labaran Kasar WAM, ya ce, kayayyakin sun hada da irinsu shinkafa, nama, sukari da sauran kayayyakin da mafi akasari aka fi amfani da su a lokacin Azumi.

Manema labarai na Arab News sun ruwaito cewa, ma’aikatar tattalin arzikin Kasar ta ce za ta yi zagaye 420, na sa ido domin tabbatar da shagunan sun yi biyayya ga sabuwar alkawuran da suka dauka.

Marwan Al-Sboosi, darekta a ma’aikatar ya ce sun gana da ’yan kasuwa tare da gargadinsu kan karin farashin kayan masarufi a lokacin Azumin.

Kazalika, Al-Sboosi ya ce sun gana da wakilan masu sayar da kayan itatuwa da na lambu da ke kasuwanni a babban birnin kasar domin tabbatar da wadatar hajarsu a lokacin watan mai tarin falala.

Alkalumma sun nuna cewa, a cikin watan Azumi kadai, ana amfani da akalla tan 17,000 na kayan itatuwa da na lambu duk rana a Dubai, yayin da kuma ake amfani da tan 5,000 a Abu Dhabi, babban birnin kasar.

A halin yanzu, ’yan kasuwa sun wadata kasar da tan dubu 130 na kayan itatuwa da na lambu yayin da ya rage sauran ’yan kwanaki kalilan a fara Azumin watan Ramalana.

(Daga jaridar Aminiya)

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!