Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ba dai dai ba ne yiwa yara katin zabe- Farfesa Riskuwa Arabu

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa shiyyar Kano ta ce ba dai dai ba ne yiwa yara kanana katin zabe domin su kada kuri’a.

Shugaban hukumar Farfesa Riskuwa Arabu Shehu ne ya bayyana hakan ga tashar Freedom Radio.

Ya ce hukumar su za ta samar ingantaccen kayayyakin aiki domin tabbatar da sahihin zabe a 2023 mai kamawa

Ya kuma ce ” hukumar ta samar da na’urar bibiyar kayayyakin zabe masu karfi da za su tantance masu jefa kuri’a”.

Riskuwa ya kara cewa” don muna so mu samar da sahihin zabe ne ma yasa muka fitar da Dabarar yin rajista katin zabe ta hanyar internet”.

Inda yace za su kuma samar da tsaro a gun zabe musamman a wajen da ake zaton akwai bata gari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!