Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Da ɗumi-ɗumi: An ɗage shari’ar Ɗansarauniya saboda ta Abduljabbar

Published

on

Kotun majistiri mai lamba 58 ta ɗage zamanta na gobe Alhamis 3 ga watan Fabrairu a kan zargin da ƴansanda ke yiwa tsohon Kwamishinan Ayyuka Injiniya Mu’azu Magaji Ɗansarauniya saboda shari’ar Malam Abduljabbar Kabara.

Mai Shari’a Aminu Gabari ne ya ɗage zaman daga 3 ga wata zuwa 4 ga watan na Fabrairu sakamakon yanayin tsaro kuma a ranar  3 ga watan ne za a ci gaba da Shari’ar Abduljabbar Nasiru Kabara.

Kotun ta yi la’akari da cewar ana jibge jami’an tsaro a Shari’ar Abduljabbar haka zalika ita ma Shari’ar Ɗansarauniyar tana buƙatur a jibge jami’an tsaro.

Ana dai zargin Ɗansarauniyar da laifin cin mutuncin gwamnan Kano Dr Abdullahi Ganduje ta hanyar yaɗa wani hoto a shafinsa na Facebook.

Wakilin Freedom Radio Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewar kotun za ta bayyana matsayarta kan roƙon da lauyan kariya ya yi na neman beli a ranar 4 ga wata maimakon 3 ga wata da aka sanya da farko.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!