Connect with us

Labarai

Ba ma fargabar matakan Trump na ƙaƙaba haraji- Shugaba Tinubu

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya bayyana cewa ƙasar nan ba ta fargabar matakan da shugaban Amurka Donald Trump ke ɗauka na ƙaƙaba haraji wanda tuni duniya ta fara ganin tasirinsa bayan haddasa naƙasu ga tattalin arziƙin ƙasashe.

 

Shugaba Bola Tinubu ya kara da cewa, kuɗaɗen da Najeriya ke samu a ɓangaren da ba na man fetur ba kaɗai, sun isa su riƙe ta tare da ƙalubalantar duk wasu haraji da Amurkan ka iya lafta wa Najeriya.

 

Tun bayan hawansa karagar mulki, shugaba Trump na Amurka, ya gabatar da sabbin harajin kasuwanci da suka birkita hada-hadar ƙasashe da dama, ciki har da Najeriyar, lamarin da Bola Tinubu ke cewa sam ba zai yiwa ƙasar illa kamar yadda ake hasashe ba, domin kuwa ƙasar na da tarin ɓangarorin da za su kangeta daga ganin tasirin harajin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!