Labarai
Ba mu kai samame gidan Obasanjo ba- EFCC

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa, EFCC, ta musanta zargin da ake yi na cewa ta kai samame a tsakiyar harabar Dakin Karatu na tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, a jihar Ogun tare da kama mutane 93 da ake zargi da damfara ta yanar gizo.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale, ya ce wadanda aka kama suna cikin wani otal da ke makwabtaka da dakin karatun. Ya ce samamen ya biyo bayan sahihin bayanin leken asiri da ya nuna cewa wadanda ake zargin sun shirya gudanar da wani taro da ya saba da doka.
EFCC ta ce tana kan bakanta cewa matakin da ta dauka bai shafi dakin karatun kai tsaye ba, sai dai yana da nasaba da miyagun ayyuka da ke faruwa a kusa da wurin.
A baya dai, shugabannin Dakin Karatun sun bukaci EFCC da ta biya su diyya ta naira biliyan 3.5
You must be logged in to post a comment Login