Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Na baiwa fadar shugaban kasa kadarorin da ake zargi na – Magu

Published

on

Dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC Ibrahim Magu, ya ce, hukumar EFCC ta bai wa hukumomin gwamnati dama fadar shugaban kasa kadarorin da ake zargin shi da wawushesu domin gudanar da aikin gwamnati bisa umarnin shugaban kasa.

Ibrahim Magu ya bayyana hakan ne ta cikin wata wasikar kariya da ya rubutawa kwamitin shugaban kasa da ke gudanar da bincike akan zarginsa da karkatar da mafi yawa na kadarorin da aka kwato daga wajen barayin gwamnati.

Tun farko dai an kama Ibrahim Magu tare da gurfanar da shi gaban kwamitin shugaban kasa karkashin jagorancin tsohon shugaban kotun kolin kasar nan, mai shari’a Ayo Salami, sakamakon zarginsa da attorney janar na kasa kuma  ministan shari’a Abubakar Malami yayi na cewa ya karkatar da dama daga cikin kadarorin da aka kwato daga wajen barayin gwamnati.

Ibrahim Magu y ace motoci da sauran kadarorin da kotu ta mallakawa gwamnatin tarayya wadanda aka kwato daga wajen barayin gwamnati an mikasu ne ga hukumomi da sassan gwamnati har ma da fadar shugaban kasa don amfani gwamnati.

Haka zalika an zargi Ibrahim Magu da ajiye kudaden a asusu yana karbar ribar da ake samu na kudaden lamarin da dakataccen shugaban hukumar na EFCC ya musanta.

Ta cikin wasikar dai Ibrahim Magu y ace tunda ya zama shugaba a hukumar EFCC har zuwa ranar da aka dakatar da shi bai taba sayar da kadarar da hukumar ta kwato daga wajen gwamnati ba ko guda daya.

Dakataccen shugaban hukumar ta EFCC y ace gaskiyar lamari duk kadarorin da hukumar ta kwato daga wajen barayin gwamnati sunanan ba wanda ya tabasu sai dai wadanda shugaban kasa y aba da umarnin mikasu ga wasu hukumomin gwamnati don amfani da su.

Haka kuma Ibrahim Magu ta cikin wasikar da ya rubutawa kwamitin na shugaban kasa da ke bincikar zargin sa da almundahanar, ya ce in ban da manyan motoci guda dari biyu da arba’in da hudu wanda babbar kotun tarayya da ta ba da umarnin sayarwa tare da hadin gwiwar hukumar kula da albarkatun man fetur ta kasa DPR babu wata kadarar da aka sayar a hukumar.

Ya kara da cewa manyan motocin da aka sayar an sanya kudadensu a wani asusun tarayya da ke babban bankin kasa kamar yadda gwamnati ta bukata.

Dakataccen shugaban hukumar ta EFCC ya bayyana wasu daga cikin ma’aikatau da hukumomi da kuma sassan gwamnati da suka amfana da kadarorin da aka kwato wanda gwamnati ta bada umarnin a basu sun hada da: ma’aikatar kula da jinkai dakile ibtila’I da ci gaban al’umma.

Sauran suner: fadar shugaban kasa da hukumar kula da ‘yan gudun hijira da wadanda rikici ya raba da gidajensu da hukumar tattara haraji ta kasa FIRS da kuma hukumar samar da aikinyi ta kasa NDE.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!